Labarai
Muna yaki da da yin bahaya a gefen hanya don tsaftace mahalli – Gwamnan Kwara
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da shirin tsaftace jihar ta hanyar yaki da yin bahaya a sarari a gefe daya kuma tare da samar da muhalli mai kyau a fadin jihar.
Gwamnan jihar AbdulRahman Abdulrazaq, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kaddamar da shirin a jiya Litinin, mai taken tsaftace jihar Kwara wato ‘Clean Kwara’ a cikin bikin shirye- shiryen cigaba mai dorewa karo na biyar.
Gwamnan ya kara dacewa hakan na daya daga cikin manufofin gwamnatin jihar wanda aka yi katari yazo dai -dai da lokacin da ake bikin cigaba mai dorewa, wanda a ciki kudurin sa na shida ya tabbatar da manufar ta samar da tsaftataccen ruwan sha da muhalli mai kyau, da kawar da bahaya a fili zuwa shekara ta 2030.
A baya -bayan nan dai bincike na kasa da aka wallafa a shekarar 2018, jihar Kwara ta kasance jiha ta 30 a cikin jihohi 36 na kasar nan da ake da tsaftataccen ruwan sha da hanyar samar da shi.
You must be logged in to post a comment Login