Labarai
NDLEA ta ɓankaɗo wadanda ke ɓata mata suna.
Hukamar Hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA ta ce ta gano ma’aikatanta biyu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a nan Kano.
Shugaban hukamar a nan Kano, Isa likita Muhammad ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan Freedom Radio.
Ya ce hukumar ta su ta dauki matakin ladaftar da su domin ya zama izna ga sauran ma’aikata hukumar da ma sauran mutanen gari.
Shugaban ya ce yanzu haka ma’aikatan hukumar na shakkar gudanar da wani aikin da ya saɓawa dokokin hukumar don gudun fuskantar hukunci.
Isa Likita ya ce ƙyamatar waɗanda suka kama shi ne ke ƙara mayar da su ruwa bayan fitowarsu,a don haka ya ke ƙara yin kira da jan su a jiki.
Shugaban hukumar NDLEA a nan Kano Isa likita Muhammad ya ce al’ummar gari na basu gudunmawa wajan bada bayanan sirri ga ɓata gari.
You must be logged in to post a comment Login