Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Munyi murna da nasarar jihar Kano a wasanni-Oba Yoruba Kano

Published

on

Sarkin Yarabawa(Yoruba ), Mazauna jihar Kano Muritala Alimi Otisese , ya yabawa tawagar jihar Kano data dawo daga bikin wasanni na ƙasa karo na 21 da aka kammala a jihar Delta mai taken Delta 2022.

Sarkin ,ya ce ƙoƙarin da jihar ta Kano tayi a gasar abin alfahari ne ,kuma tilas a yaba dashi.

Ta cikin sanarwar da sarkin ya fitar a daren Litinin , Sarkin ya ce ƙoƙarin na jihar Kano ya nuna ƙwazon ‘yan wasan jihar a ɓangare guda kuma ya jaddada matsayin jihar Kano a mataki na ɗaya daga jihohin Arewa, har ma da ƙasa baki ɗaya.

A cewar Alhaji Muritala Alimi, samun nasarar lashe Zinare 19, da kuma Azurfa 27 tare da Tagulla 30, da ya kai adadin lambobi 76 ba ƙaramar Nasara ba ce a gasar.

” Mun godewa Allah da nasarar, haka zalika mun godewa gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, kana godiya ta musamman ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, da yake babban masoyi a harkokin wasanni, da tafarkin sa muma muke bi.

Haka zalika muna yabawa shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, Alhaji (Dr), Ibrahim Galadima, da sauran ma’aikatan sa domin bisa jagorancin sa ake ta samun nasara a harkokin wasanni a jihar Kano ” inji Sarki Muritala Alimi Otisese.

Sarkin na al’umman Yarabawan Kano , ya kuma roki al’ummar jihar Kano musamman ma matasa dasu yi kokari su karbi katin su na zaɓe domin zaben shugabanni na gari a babban zaben shekarar 2023, dake ƙara karatowa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!