Addini
Musabakar alkur’ani na kara zaburar da dalibai – Shiekh Umar Fagge
Fitaccen malamain addinin musulunci anan Kano Sheikh Umar Sani Fagge ya bayyana musabakar alkurani mai girma a matsayin abinda ke nesanta al’umma daga duhun jahilci da kuma kara habbaka addinin musulunci.
Sheikh Umar Sani Fagge ya bayyana hakan ne a yau yayin da yake gabatar da mukala a taron musabakar alkurani ta kasa da aka gudanar a jami’ar Bayero da ke nan Kano.
Sheikh Fagge ya ce, musabakar alqurani na taimakawa wajen kara zaburar da dalibai da kuma sanya soyayyar karatun alkur’ani a zakatan daliban.
Da yake jawabi gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnati na shirin bude dakin karatu na musamman ga daliban islamiyya, tare da sanya na’urorin da za su saukakawa dalibai bincike.
Musabakar itace karo na 35 wanda kuma gwamnatin Kano ce ta dauki nauyin gudanar da ita.
You must be logged in to post a comment Login