Kiwon Lafiya
Mutane 1,205,87 ne suka yi rijistar JAMB a cikin kwanaki 26 da farawa
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya JAMB ta ce cikin kwanaki 26 da fara yin rijistar jarrabawar ta yiwa akalla mutane miliyan daya da dubu dari biyu da biyar, da dari da tamanin da bakwai rijista.
Shugaban hukumar shirya jarrabawar ta JAMB Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan ya yin zantawa da manema labarai jiya a Abuja.
Ya kuma ce za a fara gudanar da jarrabawar ta bana ne a ranar Asabar 16 ga watan maris zuwa ranar 23 ga watan na maris, ya kuma kara da ce zuwa Yanzu haka jihohin Kaduna da Lagos ne ke da yawan daliban da suka yi rijistar jarrabawar ta bana.
Shugaban hukumar ta JAMB Ya kuma gargadi daliban da za su rubuta jarrabawar a bana da cewar duk dalibin da na’urar tantance yatsa bata tantance su ba, ba za su shiga dakin rubutar jarrabawar.
Haka kuma hukumar ta JAMB ta ce lambar wayar da daliban ke amfani da ita da lambar sirri da ake turowa da daliban yayin yin rijistar za suyi amfani da su ne kawai yayin jarrabawar, kuma wani dalibi ba zaiyi amfani da Lambar wayar da wani ya yi amfani da ita ba yayin rijistar.