Ƙetare
Mutane 13 sun mutu a harin da Rasha ta kai Ukraine

Aƙalla mutum 13 ne aka kashe a jerin hare-haren da Rasha ta kai wa wasu biranen Ukraine ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami.
Magajin garin Kyiv, Vitali Klitschko ya ce an kashe mutane huɗu a babban birnin ƙasar, sannan an raunata fiye da hamsin, ciki har da yara da dama.
Wakilin BBC ya ce magajin garin Kyiv ya kuma ce an kai wa wani asibiti hari, lamarin da ya sa wani ɓangare na ginin rugujewa.
Hukumomin birnin Dnipro da ke gabashin ƙasar sun ce mutane tara ne suka mutu a hare-haren da aka kai a can.
Tun farko shugaba Zelensky ya ce bayanan sirri sun nuna cewa Rasha na shirin kai wa ƙasarsa gagarumin farmaki.
You must be logged in to post a comment Login