Addini
NAHCON zata fara dawo da Al’hazan Najeriya a gobe laraba

Hukumar kula d aikin hajji ta kasa NAHCON ta ce za a fara jigilar mahajjatan kasar nan daga gobe Laraba.
Shugaban Sashen Kula da Jiragen Sama na NAHCON, Alhaji Habib Bello, ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Makkah.
Bello ya ce kamfanonin jiragen sama ne suka tantance jadawalin tashi kuma Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ta amince da hakan.
A cewarsa, jirin Max Air zai fara jigilar dawowa a ranar 3 ga watan Yuni tare da mahajjata daga jihar Nasarawa, yayin da Flynas da Air Peace za su fara aiki a ranar 4 ga watan Yuni tare da mahajjata daga jihohin Ogun da Oyo.
You must be logged in to post a comment Login