Labarai
Majalisar Dattawa ta yi Allah-wadai da sace Dalibai a Oyo

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi Allah-wadai da sace ɗalibai da malamai da aka yi a jihar Oyo, tana mai bayyana lamarin a matsayin mummunan hari ga makomar ƙasa da kuma ɗan’adam baki ɗaya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana haka a ranar Talata yayin da majalisar ta koma zaman aiki bayan hutun Sallah. Ya jagoranci sanatoci yin tsayuwar minti ɗaya domin girmama malamai biyu da ɗalibi guda da suka rasa rayukansu sakamakon harin.
Akpabio ya ce rashin tsaron da ya shafi makarantu barazana ce ga makomar Najeriya, yana mai jaddada cewa gwamnati da jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane. Ya kuma miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan da gwamnatin jihar Oyo.
Haka kuma, shugaban majalisar ya gargaɗi ‘yan siyasa da masu neman muƙamai da kada su yi amfani da wannan ibtila’i wajen neman farin jini na siyasa, yana mai cewa matsalar tsaro ba ta bambanta jam’iyya, addini ko ƙabila, domin hari ne da ake kai wa Najeriya baki ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login