Labarai
Mutane 13 sun rasa rayukan su a wani mumunan hadarin mota a Kwara
Hukumar kare hadurra ta kasa, FRSC ta tabbatar da rasuwar mutane 13 a wasu hadurra guda biyu da suka faru jiya Alhamis kan titin Oloru-Bode Sa’adu da ke Ilorin babban birnn jihar Kwara.
Kwamandan hukumar shiyyar, Jonathan Owoade ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce hadurran sun faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da kuma tukin ganganci da direbobin ke yi.
Ya kara da cewa, a hatsari na farko mutane goma sha daya ne cikin fasinjoji 19 suka rasu nan-take, sannan karin mutum daya ya ya rasu a asibiti, yayin da mutane bakwai kuma suka samu raunuka.
Ya ce hatsari na biyu kuma ya faru ne sakamakon fashewar tayar motar wani mutum cikin mutane takwas da ke cikin motar ya rasu yayin da sauran suka samu raunuka.
Kwamandan FRSC ya ce tuni aka mika gawar wadanda suka rasu zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin, inda kuma ake ci gaba da kulawa da wadanda suka samu raunukaa asibitin.
You must be logged in to post a comment Login