Ƙetare
Mutane 15 sun rasu sakamakon harin jirgin yaki maras matuki a Sudan

Rahotanni daga kaar Sudan, sun bayyana cewa mutane 15 ne suka rasu sakamakon wani harin jirgin yaki maras matuki da ya auku a wata kasuwa da ke birnin El-Fasher.
Wani ma’aikacin lafiya a asibitin birnin ya shaida wa manma labarai cewa wasu mutane 12 sun jikkata sakamakon harin.
Sai dai masu rajin kare hakkin Dan-adam a yankin sun zargi dakarun RSF da kai harin.
El-Fasher shi ne birni na ƙarshe a yammacin Darfur da ke ƙarƙashin ikon sojojin gwamnati, inda aka shafe fiye da shekaru biyu suna gwabza yaƙi da dakarun RSF.
Kawo yanzu, kimanin dubban mutane ne suka mutu a rikicin da kasar Sudan ke fama da shi, yayin da miliyoyi suka rasa muhallansu.
You must be logged in to post a comment Login