Labarai
Mutane 232 sun rasu sanadiyyar ambaliyar ruwa- NEMA
Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeiya NEMA, ta ce, aƙalla mutane 232 ne suka rasu sanadiyyar ambaliyar ruwa daga watan Janairu zuwa Satumban shekarar nan da muke ciki ta 2025 a fadin Najeriya.
Ta bayyana hakan ne ta cikin wani rahoto da ta fitar, wanda kuma ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta shafi sama da mutane dubu 339 tare da lalata gidaje fiye da dubu 42.
NEMA ta kuma ce, mutane sama da dubu 121 ne suka rasa matsugunansu sakamakon wannan iftila’i.
A cewar rahoton, jihohin da iftila’in ambaliyar ta bana ta shafa sun hadar da Abia da Adamawa da birnin tarayya Abuja sai Akwa Ibom da Anambra da Bayelsa da Borno da Cross River da Delta da kuma Edo.
Sauran sun hada da Gombe da Imo da Jigawa da Kaduna da Kano da Kogi da Kwara sai Lagos da Nassarawa da Neja da Ondo da Rivers da Sokoto da kuma Taraba.
Hukumar ta kuma ce ambaliyar ta lalata gonaki a faɗin Najeriya da girmansu ya kai Kadada dubu 48, inda kuma mutane 115 suka yi ɓatan dabo da har yanzu ba a gan su ba.

You must be logged in to post a comment Login