Connect with us

Labarai

Mutane 3 sun jikkata yayin da shaguna suka kone sakamakon gobarar motar dakon Gas a Zaria

Published

on

Mutane uku sun jikkata yayin da wasu shaguna suka kone  Kurmus sakamakon tashin gobara a wata motar dakon gas a yankin Kwangila da ke Karamar Hukumar Zaria ta  Jihar Kaduna.

 

Hakan  na kunshe a  cikin sanarwar da hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC reshen jihar ta fitar.

 

Sanarwar ta ce motar wadda ke dauke da iskar gas ta kama da wuta ne yayin da take ajiye a gefen hanya a kan hanyar Funtua zuwa Zariya.

 

Haka zalika  ta ce gobarar ta shafi shagunan da ke kusa tare da jikkata mutane uku da aka kai asibiti domin samun kulawa.

 

FRSC ta  ce jami’an agajin gaggawa sun samu nasarar shawo kan gobarar tare da dakile yaduwarta zuwa wasu wurare.

 

Hukumar ta bukaci masu ababen hawa da su yi taka-tsantsan yayin wucewa yankin tare da bin umarnin jami’an tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!