Labarai
Wike ya musanta zargin jam’iyyar ADC na hana ta amfani da Eagle Square

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta zargin da jam’iyyar hadaka ta ADC ta yi cewa an hana ta amfani da dandalin Eagle Square.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja yayin rangadin duba ayyukan gine-gine.
Ya ce zargin cewa an hana wasu jam’iyyu amfani da dandalin Eagle Square ba shi da tushe.
A cewarsa, babu wata buƙata a hukumance da jam’iyyar ADC ta gabatar da sunan tana son ta yi amafi da dandalin.
Ya jaddada cewa Eagle Square a buɗe yake ga dukkan jam’iyya da kungiyoyi matuƙar sun bi ka’ida kuma sun biya kudin da aka ƙayyade.
Sai dai jam’iyyar ADC ta dage cewa ta bi dukkan matakan da doka ta tanada, inda ta ce ta riga ta mika takardar buƙata domin neman amfani da dandalin. Jam’iyyar ta bayyana cewa zargin cewa ba a karɓi wata takarda daga gare ta ba ba gaskiya ba ne.
You must be logged in to post a comment Login