Connect with us

Labarai

Farashin mai ya sake tashi a kasuwar Duniya

Published

on

Farashin mai ya tashi a kasuwar Duniya bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran, da kuma sanarwar da Washington ta yi cewa za ta rufe mashigar tekun Iran baki ɗaya.

 

Farashin ɗanyen mai na Brent ya tashi da fiye da kashi bakwai cikin ɗari, inda ya kai dala 103 kowacce ganga.

 

Iran dai ta yi gargaɗin cewa za ta kai hari kan duk wani jirgin ruwan soji da ya doshi mashigar Hormuz.

 

Sa’o’i bayan alwashin Shugaba Trump na hana zirga-zirgar jiragen ruwan, rundunar sojin Amurka ta yi ƙarin haske kan batun, inda ta ce matakin zai shafi jiragen ruwa ne da kodai suka tashi daga gaɓar tekun Iran ko kuma suke kan hanyar zuwa can.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!