Labarai
Mutane 3,433 sun rasu yayin da 22,162 suka jikkata sakamakon hadurra daga Janairu zuwa Satumba- FRSC

Hukumar Kiyaye afkuwar Haddura ta Ƙasa FRSC ta bayyana cewa akalla mutane 3,433 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 22,162 suka jikkata a cikin hadurra 6,858 da suka faru a faɗin kasar nan daga watan Janairu zuwa Satumbar 2025.
Jaridar Punch ta ruwaito cewar babban Kwamandan hukumar FRSC, Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, a wajen ƙaddamar da gangamin wayar da kan jama’a na watanni hudun karshen shekarar nan.
Shugaban ya ce yawancin hadurran sun samo asali ne daga gajiya yayin tuƙi, ɗaukar fasinjoji fiye da ƙima, ɗaukar mutane a motoci na kaya, da sauran su.
Hukumar ta ce za ta ƙara tsaurara matakai ta hanyar sanya jami’ai da masu sa kai a manyan tituna, gudanar da binciken motoci kyauta, da kuma wayar da kai a tashoshin mota da tarukan jama’a.
You must be logged in to post a comment Login