Connect with us

Labarai

Mutane 48 ne suka mutu bayan haɗarin jirgin ruwa a jihar Sokoto

Published

on

Kimanin mutum 48 ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman yara 12 bayan haɗarin jirgin ruwa da ya faru a yankin Goronyo da ke jihar Sokoto.

 

Akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su yara ne waɗanda ke kan hanyar zuwa gona a safiyar jiya Alhamis.

 

A tattaunawarsa da BBC, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Gada da Goronyo a majalisar wakilan kasar nan, Bashir Gorau ya ce a halin yanzu masu ninkaya na ci gaba da aikin ceto domin ganin ko za a samo sauran yaran da suka ɓace da ransu.

 

Hatsarin kwale-kwale da ake yawan fuskanta a kasar nan, na laƙume rayukan mutane musamman a yankunan karkara.

 

Lamarin ya fi ƙamari ne a lokacin damina, inda rafuka kan cika da ruwa, sannan kuma babu wasu matakan kariya da ake amfani da su wajen irin wannan sufuri, haɗi da rashin ingancin kwale-kwalen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!