Connect with us

Labarai

EFCC ta janye ƙarar da ta shigar da wasu ɗaliban Jami’ar Bayero ta Kano

Published

on

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, ta janye ƙarar da ta shigar kan wasu ɗaliban shekarar ƙarshe a Jami’ar Bayero da ke Kano, Maryam Isah Shehu, da Abubakar Shuraim Abdulhamid.

An gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin aikata laifin yanar gizo da kuma wallafa bayanan da hukumar ta ce suna da nufin ɓata mata suna.

EFCC ta zargi Maryam da wallafa wani saƙo a kafar sada zumunta, inda ta yi zargin cewa jami’an hukumar sun ci zarafin wani mutum, bisa umarnin wani jami’in hukumar.

Sai dai shugaban hukumar ta EFCC, Ola Olukoyede, ya bayar da umarnin janye ƙarar bayan ya yi la’akari da roƙon mahaifin Maryam na neman afuwa, da kuma kiran wasu ‘yan kasa na a yi wa matasan sassauci.

EFCC ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa doka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!