Connect with us

Coronavirus

Mutane 9 ne suka kamu da cutar COVID 19 a Kano – Ganduje

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce a jiya Alhamis an sami karin mutane 9 masu dauke da cutar Covid-19 cikin mutane 120 da aka yiwa gwaji, wanda a yanzu haka mutane 1,692 ne suka kamu da cutar cikin su kuma guda 1,366 suka warke sai kuma guda 54 da suka rasa ransu dalilin cutar.

Hukumar ta kuma ce a kasa baki daya an sami karin mutane 476 masu dauke da cutar, abin da ya kara yawan masu cutar zuwa dubu 50,964 cikin su kuma an sallami mutane 37,569 yayin da 992 suka rasa rayukan su dalilin cutar.

Jihar Kaduna ta sami karin mutane 41 masu fama da cutar, inda a yanzu haka yawan masu fama da cutar a jihar ya kai 1, 923 cikin su kuma 1,674 suka warke sai kuma 12 suka hallaka dalilin cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,784 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!