Kiwon Lafiya
Mutane hudu sun rasa rayukansu sanadiyar cutar Sankarau a jihar Neja
A kalla mutane hudu ne suka rasa rayukan su a jihar Neja sakamakon barkewar cutar sankarau.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr Mustapha Jibril ne ya sanar da hakan a jiya Laraba , inda ya ce an samu rasuwar mutanen ne a karamar hukumar Katcha da kuma Magama.
A cewar kwamishinan sun samun rahotanin cewar sama da mutum 31 ne suka kamu da cutar a fadin jihar inda tara da ga ciki aka tabbatar da cutare a tare su bayan da aka yi musu gwaje-gwaje a asibiti.
Rahotannin na nuni da cewar annobar cutar ta sake komowa kasar nan, biyo bayan barkewar ta a wasu jihohin kasar nan a shekarar bara inda, ta kuma janyo asarar rayukan samma da 400 wanda mafiya yawansu sun fito ne daga arewacin kasar nan.
Inda kuma rahotannin ke nuni da cewar jihar Zamfara ita ce jihar da tafi kowacce kamuwa da cutar.