Labarai
Mutane uku sun jikkata a wani rikici na manoma da makiyaya a jihar Neja

Akalla mutane uku sun jikkata a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a garin Kataeregi, ƙaramar hukumar Katcha ta jihar Neja.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce rikicin ya samo asali ne daga takaddamar iyakar gonaki tsakanin wasu al’ummomin manoma da mazauna wani sansanin makiyaya.
Ya ce wasu matasa daga al’ummomin yankin sun kai hari kan sansanin makiyayan, lamarin da ya haddasa rikicin.
Abiodun ya ce an lalata babura hudu a yayin rikicin, yayin da ’yan sandan Kataeregi suka isa wurin tare da kai wadanda suka jikkata asibiti.
Ya ce matakin ’yan sandan ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya, yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba.
You must be logged in to post a comment Login