Labarai
Mutanen da suka mutu sakamakon Zazzabin Lassa sun karu zuwa 252- NCDC

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC, ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar zazzabin Lassa a Najeriya ya kai 252, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya karu zuwa 1,035.
NCDC ta ce an samu sabbin mutane 14 da aka tabbatar sun kamu da cutar a makon da ya gabata, inda aka gano su a jihohin Ondo, Bauchi, Edo da Benue.
Cibiyar ta ce adadin wadanda suka mutu ya karu daga 240 zuwa 252, yayin da yawan mace-macen cutar ya kai kashi 24.4 cikin 100.
Jihohin Bauchi, Ondo, Taraba, Benue da Edo ne suka fi yawan samun wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar.
NCDC ta ce tana ci gaba da sanya ido da daukar matakan dakile yaduwar cutar, wadda ke ci gaba da zama babbar barazana ga lafiyar al’umma.
You must be logged in to post a comment Login