Connect with us

Labarai

Za mu koma aiwatar da yarjejeniyar Islamabad idan Amurka ta koma cika alƙawuran da ta ɗauka- Iran

Published

on

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ƙasarsa za ta koma aiwatar da yarjejeniyar Islamabad nan take idan Amurka ta koma cika alƙawuran da ta ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar.

 

Shugaban, bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a taron Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai, Pezeshkian ya ce Iran a shirye take ta mayar da martani iri ɗaya idan Washington ta mutunta yarjejeniyar.

 

A wani ɓangaren kuma, rundunar sojin Iran ta sake gargaɗin ƙasashen yankin cewa za ta kai farmaki ga duk wata ƙasa da aka yi amfani da yankinta wajen kai mata hari.

 

Rahotanni sun kuma ce an kai hari kan wani tankar ɗanyen mai a mashigar Hormuz, yayin da Sakataren Sojin Amurka Daniel Driscoll ya yi murabus bayan samun saɓani da Sakataren Tsaro Pete Hegseth.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!