Labarai
Rundunar ’yan sanda ta tura jami’ai 250 zuwa kananan hukumomin kan iyaka Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta tura jami’ai 250 zuwa kananan hukumomin da ke kan iyakar jihar, domin karfafa tsaro da dakile matsalolin rashin tsaro.
Jami’an, wadanda suka kammala wani horo na musamman na tsawon wata guda, za su taimaka wajen gudanar da sintiri da sauran ayyukan tabbatar da tsaro a yankunan.
Rundunar ta ce matakin na daga cikin kokarinta na kara yawan jami’an tsaro a wuraren da ke da muhimmanci, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Rundunar ta kuma bukaci alumma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai, tare da kai rahoton duk wani mutum da ake zargi da barazana ga zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login