Connect with us

Addini

Na fice daga kwamitin amintattu na masallacin waje da ke Fagge – Ƙalarawi

Published

on

Guda daga cikin mambobin kwamitin amintattu na masallacin Juma’a da ke WAJE a unguwar Fagge a nan Kano Shiekh Tijjani Bala Kalarawi ya ajiye mukamin sa.

Shiekh Tijjani Bala Kalarawi ya bayyana ficewar ta sa daga kwamitin ne yayin wata ziyara da ya kawo nan Freedom Radio.

Tijjani Bala kalarawi yace ya rubutawa mai maitaba sarki Kano Alhaji Aminu Ado Bayero takardar sanar da shi cewa ya sauka daga muƙaminsa na mamba a kwamintin amintattu na massallacin.

“Nazo wucewa sai naga ana sare katangar da ta kewaye harabar masallacin ana fidda harsashin wani gini kamar yadda aka yi a masallacin idi, sai naga har an shiga cikin masallacin daga yamma ana aune aune alamu na nuna gini za a yi wanda bai shafi masallacin ba” a cewar Ƙalarawi.

Ƙalarawi ya ci gaba da cewa “Na yi ƙoƙarin samun mai yi mun bayani ga me da halin da masallacin ke ciki amma abin ya faskara, duk wanda na yiwa magana babu amsa, amma a lokacin da mai maitaba sarki Ado ya nada ni babu massallacin daya kai na Waje gata”.

Ƙalarawi ya nemi izinin mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da ya bashi damar ajiye muƙamin sa domin kuwa duk wanda aka naɗa su tare sun mutu.

Sai dai yayi zargin cewa akwai coci a kusa da masallacin amma ba a taɓa ta ba sai masallaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!