Labarai
Na yi imani Buhari ba ya bacci, tsokacin Jonathan, kan rashin tsaro a Nigeria
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya jagoranci wata tawaga ta musamman zuwa gidan gwamnatin jihar Delta da ke garin Asaba don yiwa gwamna Ifeanyi Okowa ta’aziyar mutuwar mahaifinsa.
Jonathan ya kuma shawarci shugaba Buhari da ya hadakan gwamnoni da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su rika aiki tare don kawo karshen matsaloli da kasar nan ke fuskanta a wannan lokaci.
‘‘Abin takaici ne yadda lamarin rashin tsaro ya kai a wannan lokaci kusan kullum sai anji labari marar dadi, musamman sace dalibai ‘yan makaranta don neman kudin fansa’’
‘‘Na yi Imani idan har za a samu hadin kai tsakanin gwamnoni da jami’an tsaro da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki nan ba da jimawa ba za a dakile matsalolin tsaro da ke addabr kasar nan’’
‘‘Ni a matsayina na tsohon shugaban kasa na tabbata shugaba Buhari baya bacci gwamnoni suma basa bacci da su kansu uwa uba jami’an tsaro’’ inji Jonathan.
Tsohon shugaban kasar ya kuma yabawa shugaba Buhari bisa ga yadda ya ce yana kokari tare da aiki tukuru ba dare ba rana wajen ganin an kawo karshen matsalolin tsaro.
You must be logged in to post a comment Login