Connect with us

Labarai

NAFDAC ta fara samame don tabbatar da hana sayar da ƙananan Barasa

Published

on

Hukumar Lura da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya NAFDAC, ta fara wani samame a faɗin kasar nan domin tabbatar da cikakken aiwatar da haramcin sayar da dukkan nau’ikan giya da ake zubawa a cikin leda da kuma kwalaben roba masu ƙasa da girman milimita 200.

 

Matakin ya zo ne bayan wa’adin da gwamnatin tarayya ta bayar ya kammala , inda hukumar ta ce daga yanzu za ta kama duk wanda aka samu yana samarwa, rarrabawa ko sayar da irin waɗannan kayayyaki da aka haramta.

 

NAFDAC ta bayyana cewa manufar haramcin ita ce kare lafiyar jama’a, musamman matasa, tare da rage yawan shaye-shayen giya da ke haddasa matsalolin lafiya da na zamantakewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!