Labarai
NAFDAC ta lalata jabun kayayyakin da marasa inganci na fiye da Naira Tiriliyan 1

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta NAFDAC, ta ce ta lalata kayayyakin jabu da marasa inganci da darajarsu ta haura sama da Naira tiriliyan 1, a wani samame da ta gudanar a Lagos da yankin Kudu maso Gabashin kasar nan tsakanin Fabrairu da Maris na shekarar da ta gabata 2025.
Daraktar Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce samamen da aka gudanar a kasuwannin Idumota da ke Legas, Onitsha da kuma Ariaria International Market da ke Aba, ya kai ga kwace da lalata kayayyakin jabu sama da manyan motoci 137, kowacce dauke da kwantena mai kafa 40.
Ta ce tun daga shekarar 2023 zuwa yanzu, NAFDAC ta kwace ko lalata kayayyakin jabu da marasa inganci da darajarsu ta kai sama da Naira tiriliyan 1.54 a fadin Najeriya.
Adeyeye ta kuma bayyana masu hadawa da sayar da kayayyakin jabu a matsayin ’yan kasuwar mutuwa’ tare da jaddada cewa hukumar ba za ta yi sassauci wajen yaki da jabun kayayyaki ba.
You must be logged in to post a comment Login