Connect with us

Labarai

Gwamna Abba ya raba tallafin fiye da miliyan 55 ga masu ƙananan sana’o’i

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta raba tallafin kuɗi sama da Naira miliyan 55 da dubu dari takwas ga masu ƙananan sana’o’i da masu tallace-tallace a kan tituna domin bunƙasa harkokin kasuwancinsu.

Da ya ke ƙaddamar da rabon tallafin, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa mutane 1,116 ne suka amfana, inda kowanne daga cikinsu ya samu Naira dubu hamsin domin ƙarfafa sana’o’insu

Gwamna Abba ya ce, bai wa matasan tallafin kuɗi da yawan su ya zarce naira miliyan 55 lokaci guda, zai taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’in da suke yi akan tituna da danjojin motoci a Kano tare da ɗauke hankalin su daga aikata munanan laifuka.

Gwamnan ya kuma sha alwashin ci gaba da tallafa wa masu ƙananan sana’o’i a faɗin Kano da nufin sauya tunanin matasa maza da mata a jihar daga abubuwan da basu da amfani ya zuwa yadda za su taimaka wa kansu har ma da sauran al’umma.

Wasu daga cikin matasan da aka tallafa wa sun jinjina wa yunƙurin gwamnan inda suka ba shi tabbacin cewar za su yi amfani da tallafin ta kyakkyawar hanyar musamman wadda za ta haɓɓaka tattalin arzikin Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!