Manyan Labarai
NAFDAC ta kone jabun magunguna na fiye da Naira biliyan 3 a Kano
Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta kone jabun magunguna da fataucin miyagun kwayoyi da suka kai kimar naira bilyan uku cikin shekaru biyu a jihar Kano.
Shugaban hukumar reshan jihar Kano Shaba Muhammed ya bayyana wa manema labaraia a yau Alhamis.
Muhammed ya ce sun kama magungunna a wani hadin gwiwa sumame da jamien ta suka kai a sassa daban daban a fadin jihar.
Shugaban ya kara da cewa hukumar sa ta sami gagarimar nasara wajan yaki da fataucin miyagun kwayoyi saboda yawan samun masu taamali da kwayoyi cikin shekaru goma a fadin jihar.
Ya kara da cewa a karon farko jihar Kano ta koma na shida cikin jerin jihohin da suka fi kowa amfani da miyagun kwayoyi a fadin kasar nan.
Shugaban yace hukumar ta sami nasara sakamakon hadi kai da sauran hukumomin tsaro suke bayar wa wajan yaki da fataucin miyagun kwayoy
You must be logged in to post a comment Login