Labarai
Gwamnatin Kwara ta sanar da ranar fara jigilar maniyyata Hajjin bana

Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da cewa za a fara jigilar maniyyatan aikin Hajjin shekarar 2026 daga ranar 6 ga watan Mayu mai kamawa.
Hukumar kula da aikin Hajji ta jihar ta bayyana cewa an kammala shirye-shiryen da suka haɗa da tsara jadawalin tashi, da kuma raba sabbin katinan shaida ga maniyyatan domin saukaka tantancewa da tsaro.
Haka kuma, an bukaci dukkan maniyyata su kammala duk wasu muhimman abubuwa kamar allurar rigakafi, tantance takardu, da halartar bitar horo kafin ranar tashi.
Jihar ta tabbatar da cewa za a gudanar da aikin cikin tsari da aminci domin tabbatar da jin daɗin maniyyata yayin gudanar da ibadar Hajjin bana.
You must be logged in to post a comment Login