Kiwon Lafiya
NAHCON:maniyyata su shigar da bayanansu don kaucewa shiga matsala
Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta bukaci dukkanin maniyyata aikin hajjin bana wadanda suka biya cikakkun kudaden da su duba shafukan hukumar jin dadin alhazai na jihohin su domin su tabbatar an shigar da bayanan su dai-dai domin gujewa fadawa matsala.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwar da jami’ar hulda da jama’a a hukumar ta NAHCON Fatima Usara ta fitar a jiya Laraba, inda ta ce hukumar na umartar maniyyatan da su yi wannan bibiya kafin nan da ranar 12 ga watan Yulin da muke ciki.
Haka kuma ta cikin sanarwar Fatima Usara ta ce za a fara jigilar mahajjatan daga nan gida Najeriya zuwa kasa mai tsarki kafin nan da karshen wannan wata da muke ciki.
Ta ce dukkanin maniyyatan da basu gudanar da wannan aikin binciken ba hakan zai iya shafar damar da suke da ita na gudanar da aikin hajjin na bana, duba da cewa dukkanin wadanda hukumar bata da bayanin su a shafin ta, hakan na nufin shi ba maniyaci ba ne.
Sanarwar dai ta kuma kara jaddada cewar dukkanin maniyyacin da ba a dauki baya nan sa dai-dai ba to shakka babu ba zai samu shaidar izinin shiga kasar ta Saudiyya ba.