Labaran Kano
Najeriya ba za ta taba durkushewa ba – Lai Muhammad
Ministan Yada labaru Najeriya Alhaji Lai Muhammad ya ce kasar nan ba za ta taba durkushewa ba har’abada, duk kuwa da mummunar fatan da’ake mata ko ta ko ina.
A watan Disambar bara jaridar Financial times ta Birtaniya ta wallafa cewa Najeriya na kan gabar wargajewa saboda yawan garkuwar da ake yi da jama’a da kuma ta’asar da barayin daji ke yi a kasar.
Sai dai a wani taron manema Labaru Ministan ya yi tur da wannan labari, yana mai cewa gwamnati na samun nasara a yakin da ta ke yi da masu aikta miyagun laifuka.
“Ya ce ba tun yanzu ba ake hasashen wargajewar kasarnan, amma hakan bai yuwuba kuma bazai taba yuwu din ba sam-sam”
You must be logged in to post a comment Login