Kiwon Lafiya
Najeriya ce kan gaba a yawan yara masu cutar Yunwa a Afirka- UNICEF

Asusun tallafa wa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce, Najeriya ce kasar da ta fi kowacce yawan yara masu fama da cutar karancin abinci mai gina jiki da ake kira da Tamowa a kaf nahiyar Afirka.
Asusun ya bayyana hakan ne a shafin sa na yanar gizo a ranar Talata, inda ya kara da cewa yara biyu cikin duk guda 10 na fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Haka kuma, ya kara da cewa, kimanin yara miliyan biyu ne ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a Najeriya, kuma ita ce kasa ta biyu a yawan kananan yara a duniya masu dauke da cutar ta Tamowa.
You must be logged in to post a comment Login