Labarai
Ministan Ilimi zai dauki mataki kan yan kwangilar da ke gina babban dakin Karatu na kasa

Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa, ya yi barazanar daukar matakin hukunci kan ’yan kwangila da masu ba da shawara da ke aikin gina babban dakin Karatu na kasa, saboda jinkirta aikin.
Dakta Alausa ya bayyana hakan ne a Abuja, yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan aikin.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta samar da kudin da ake buƙata domin kammala aikin, amma dole ne ’yan kwangilar su tabbatar da inganci da kuma kammala aikin a cikin wa’adin da aka kayyade.
Ministan ya ce za a raba aikin zuwa sassa biyu, inda za a gudanar da aikin ginin da kuma samar da kayan dakin a lokaci guda.
Ya kuma ce an sake tsara dakin karatun ne bisa tsarin babban dakin Karatu na kasa na Qatar, domin ya dace da zamani.
A cewarsa, sabon tsarin zai tanadi wurare na musamman ga yara, masu bukata ta musamman, mata masu juna biyu da matasa.
An fara aikin ginin Babban dakin karatu na kasa a Abuja a shekarar 2006, amma aikin ya tsaya bayan shekaru biyu, yanzu gwamnatin tarayya ta sake daukar matakin ganin an kammala shi.
Ministan ya ce gwamnati za ta bukaci ’yan kwangilar su yi aiki yadda ya kamata, domin tabbatar da cewa aikin bai sake fuskantar jinkiri ba.
You must be logged in to post a comment Login