Connect with us

Labarai

Gwamna Makinde ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa nasarar ceto ɗalibai da malaman jihar

Published

on

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya miƙa godiyarsa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da jami’an tsaron Najeriya bisa nasarar ceto ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jihar.

Makinde ya bayyana hakan ne a yayin shirin Politics Today na tashar Channels Tv a ranar Juma’a,
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar na amfani da wannan dama wajen nuna godiya ga dukkan jami’an tsaro da kuma Shugaba Tinubu saboda ƙoƙarin da suka yi domin tabbatar da nasarar aikin ceton.

Kalaman Makinde na zuwa ne bayan jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su, bayan sun shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!