Labarai
Najeriya ta dakatar da ziyarar ibada zuwa Isra’ila

Hukumomi a Najeriya sun dakatar da dukkan ziyarar ibada zuwa ƙasar Isra’ila nan take, sakamakon matsalolin tsaro da ke tasowa daga rikicin da ke ƙara ta’azzara a Gabas ta Tsakiya.
Sanarwa da hukumar shirya ziyarar ibada ta Kristoci ta fitar ta ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da “lafiya da jin daɗin” matafiya ‘yan Najeriya.
Dakatarwar ta shafi duk ziyarar ibada da hukumomin gwamnati da na masu zaman kansu ke shiryarwa kuma za ta ci gaba har sai an samu kwanciyar hankali a yankin.
Dubban ‘yan Najeriya Kiristoci na zuwa Birnin Ƙudus da Bethlehem da Nazareth duk shekara don ziyarar ibada.
Wannan ziyarar addinin suna da muhimmanci a kalandar addinin Kiristoci ta Najeriya.
Najeriya, ƙasa mafi yawan mutane a Afirka, na da yawan Kiristoci musamman a kudu, kuma ziyarar ibada zuwa Isra’ila na da matuƙar muhimmanci ga masu bin addinin Krista, inda da yawa ke tattara kuɗi na tsawon shekaru don yin ziyarar.
Hukumomin Najeriya ba su bayyana lokacin da za a soke dakatarwar ba, amma sun ce suna sa ido sosai kan halin da ake ciki.
Ba wannan ne karo na farko da ake dakatar da ziyarar ibada ba saboda tsaro.
A yanzu, an shawarci masu shirin zuwa ziyarar da su jira ƙarin bayani daga hukumomin ƙasar masu ruwa da tsaki.
You must be logged in to post a comment Login