Kiwon Lafiya
Najeriya ta rasa yan kasar ta guda biyu a hatsarin jirgin saman kasar Ethopia
Majalisar dokoki ta kasar Habasha ta sanar da zaman makoki kwana guda bayan jirgin kasar kirar Boeing 737 yayi hatsari da ya taso daga kasar ya nufi kasar Kenya.
Fasinjoji fiye da 30 ne a cikin sa ciki har da ma’aikatan majalisar dinkin duniya 19.
Sauran su ne akwai masana da likitoci da malaman jami’I’o har fa da fitaccen marubucin nan na kasar nan Pius Adesanmi dake kasar Kanada na cikin jirgin
Haka zalika firaministan kasar Slobakiya Anton Hrnko ya tabbatar da cewar, mai dakin sa da ‘ya’yan sa biyu na cikin jirgin. Har ila yau firaministan kasar Ethopia Abiy Ahmed yayi alkawarin wallafa dalilan da suka sanya jirgin ya yi hadari