Kiwon Lafiya
Najeriya ta sauka a matsayi na 146 a jerin Kasashen da suka fi saukin gudanar da kasuwanci
Najeriya ta sauko matsayi na 146 daga matsayin da ta ke na 145 a shekarar da ta wuce, a jerin kasashen duniya da aka fi saukin gudanar da kasuwanci.
Rahoton da bankin duniya ke fitarwa a duk shekara wanda aka fitar a jiya Laraba, ya ce, an yi amfani da manufofi da gwamnatocin kasashe ke fitarwa har guda 314 a kasashe 128 wajen fitar da sakamakon rahoton.
Da ya ke Karin haske kan batun shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim, ya ce, wajibi ne gwamnatoci su bullo da sabbin tsare-tsare da za su saukaka harkokin kasuwanci a kasashen su.
Haka kuma rahoton na bankin duniya ya kuma ce a yankin kasashen afurka da ke kudu da hamadas-Sahara an gudanar da sauye-sauye guda dari da bakwai, lamarin da bankin na duniya ke cewa abin a yaba ne.
A cikin rahoton na bankin na duniya, ya kuma ce, Najeriya ta gudanar da sauye-sauye guda hudu, ciki har da wani shirin fara kasuwanci a saukake a jihohiin Kano da Lagos.
Sai dai a cewar shugaban bankin na duniya, Jim Yong Kim, akwai bukatar kara kokari wajen gudanar da sauye-sauye da za su saukaka hanyoyin kasuwanci.