Kiwon Lafiya
Nan da kwanaki 15 idan gwamnati bata biya mana bukatun mu ba zamu fara yajin aiki-JOHESU
Gamayyar kungiyoyin ma’aiktan lafiya na Najeriya JOHESU sun bawa gwamnati wa’adin kwanaki 15, kan ta biya musu bukatun su ko su tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani.
Shugaban kungiyar Kwamared Biobelemoye Josiah, ne ya fadi hakan a cikin wata wasika da ya aike wa Ministan Kwadago Sanata Chris Ngige, da sauran masu ruwa da tsaki yau Asabar a Abuja.
Josiah ya ce, matukar wa’adin kwanaki 15 ya cika gwamnati ba ta biya musu bukatun su ba, ya zama dole su tafi yajin aiki duba da halin da membobinsu ke ciki.
Wannan na zuwa ne bayan yajin aikin da Likitoci masu neman kwarewa ke yi da kuma wa’adin kwanaki 21 da Kungiyar Likitoci ta kasa ta ba gwamnatin tarayya don fara yajin aikin gama gari a duk fadin kasar.
You must be logged in to post a comment Login