Labarai
NBMOA ta nada shugaban tashoshin Freedom Radio a matsayin shugabanta na riko
Kungiyar mamallaka kafafen yada labarai ta Arewacin kasar nan ta kaddamar da kwamitin rikon da zai jagoranci babban taronta na shekara-shekara tare da zabar sababbin shugabanni.
kungiyar ta nada Alhaji Abbas Muhammad Dalhatu, shugaban rukunin tasoshin Freedom Radio da Dala Fm a matsayin shugaban kwamitin rikon.
Sai Hajiya Maimuna Yahya shugabar gidan rediyon WE FM a matsayin sakatariyar kwamitin.
A jumma’ar data gabata ne shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Dakta Ahmad Tijjani Ramalan ya kaddamar da kwamitin rikon a birnin tarayya Abuja.
Wannan na zuwa ne bayan karewar wa’adin tsoffin shugabannin kungiyar wanda shugaban tasoshin Unity Radio da Talabijin Alhaji Salihu Dasuki Nakande ya jagoranta.
Ana sa ran kwamitin rikon zai tsara yadda za a iya gabatar da babban taron kungiyar na shekara-shekara da yin zabe ido da ido ko kuma ta hanyar fasahar zamani.
Sannan kwamitin rikon zai samar da shawarwarin da za a yi gyare-gyare a kundin tsarin mulkin kungiyan.
Rahoton: Bashir Sharfadi
You must be logged in to post a comment Login