Connect with us

Labarai

NDC za ta daukaka kara kun hukuncin da ya soke rajistar Jam’iyyar

Published

on

Jam’iyyar NDC ta sanar da cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke, wanda ya soke hukuncin da ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta yi mata rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.

A cikin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Moses Cleopas Zuwoghe, ya sanya wa hannu, NDC ta bayyana cewa ba ta gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba, tana mai cewa ƙungiyar Peace Movement Party (PMP), wadda ta shigar da ƙarar, ba jam’iyya ce mai rijista ba, kuma ba ta cikin masu neman rajista a halin yanzu.

Jam’iyyar ta ce tun a watan Disamban shekarar 2025 ne kotu ta ba ta damar kafa jam’iyya tare da umartar INEC ta yi mata rajista, lamarin da ta ce hukumar ta aiwatar.

NDC ta ƙara da cewa tun bayan samun rajistar, ta gudanar da rajistar mambobi, ta kafa shugabanci daga matakin mazaɓu zuwa na ƙasa, sannan ta shiga wasu zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a jihohin Nasarawa da Enugu.

Sai dai jam’iyyar ta bayyana cewa hukuncin da kotun ta yanke bai soke rijistarta kai tsaye ba, sai dai ya soke hukuncin da ya tilasta wa INEC yi mata rajista.

A ƙarshe, NDC ta ce ta umarci lauyoyinta da su garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!