Connect with us

Labarai

Kotu ta soke rajistar jam’iyyar NDC

Published

on

Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta yi wa jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.

Kamfanin dillancin labarai na NAN, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, ya ruwaito cewa Mai Shari’a Isah Dashen ya yanke hukuncin ne ranar Juma’a, inda ya bayyana cewa dole ne a bai wa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa damar kare kansu kafin a yanke hukunci kan shari’ar.

Mai shari’ar ya amince da buƙatar jam’iyyar Peace Movement Party PMP, yana mai cewa jam’iyyar tana daga cikin waɗanda shari’ar ta shafa, ya ce hukuncin da aka yanke a watan Disambar 2025 ya saɓa wa kundin tsarin mulki domin an yanke shi ba tare da sauraron dukkan ɓangarorin da abin ya shafa ba.

Kotun ta kuma umarci a mayar da komai yadda yake kafin hukuncin ranar 10 ga Disamba, 2025, har sai an sake sauraron shari’ar gaba ɗaya, haka kuma, ta ce an ɓoye wasu muhimman bayanai a lokacin shari’ar farko, lamarin da ya sa aka soke hukuncin.

Bugu da ƙari, kotun ta umarci a sake fara sauraron shari’ar daga farko tare da haɗa INEC, PMP da kuma NDC a matsayin ɓangarorin da za su halarta domin a tabbatar an yi adalci ga kowa.

Lauyan PMP, Chikezie Ekeocha, ya bayyana cewa sun garzaya kotu ne bayan sun gano cewa tambarin da aka yi wa NDC rajista da shi ya yi kama da wanda PMP ta gabatar wa INEC tun kafin fara shari’ar.

Ya ce hukuncin yana nufin an soke duk wani mataki da INEC ta ɗauka bisa tsohon hukuncin, ciki har da ba wa NDC takardar rajista da saka sunanta cikin bayanan hukumar, har sai an kammala sabon sauraron shari’ar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!