Connect with us

Labarai

An gurfanar da ƙarin mutum 17 kan zargin kisan wata mata a maraban Jos

Published

on

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta sanar da gurfanar da wasu ƙarin mutane 17 da ake zargi da hannu a kisan gayyan da aka yi wa wata mata a Ungwar maraban Jos, na jihar Kaduna a makon da ya gabata.

Wata sanarwar da ta fito daga ofishin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Mansir Hassan ta ce an gurfanar da waɗanda ake zargin ne yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Sabarwar ta ƙara da cewa bayan kammala binciken farko, an gurfanar da wasu mutane talatin da uku (33) da ake zargi da laifin haɗa baki da kuma yin taro ba bisa ƙa’ida ba.

Rundunar ta kuma bayyana cewa mutane talatin (30) da aka kama bayan aukuwar lamarin, ba same su da hannu wajen aikata laifin ba, kuma an sake su ba tare da wani sharaɗi ba.

Rundunar ta sake nanata cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda ta bayar da tabbacin cewa ta na ƙara ƙaimi wajen ganowa da kamo duk waɗanda ke da hannu, ko kuma suka taimaka wajen aikata wannan laifi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!