Labarai
NDLEA ta kama manyan harsasai guda 380 a tare da cafke ma’aurata da tabar wiwi ta miliyoyi

Hukumar hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce, ta kama manyan harsasai guda 380 irin na sojoji a Jihar Kaduna, tare da cafke wasu ma’aurata da ake zargi da mallakar tabar wiwi mai nauyin sama da tan 1.2.
Daraktan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na hukumar, Femi Babafemi, ne ya sanar da hakan ga manema labarai.
Ya kuma ce, jami’an NDLEA sun kama wani mutum mai shekaru 30 mai suna Sunusi Musa a ranar 24 ga watan Mayu yayin sintiri a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a yankin Jere, inda ake zarginsa da jigilar harsasan zuwa Jihar Katsina.
Sanarwar ta ƙara da cewa an miƙa wanda ake zargin tare da harsasan da aka ƙwato ga hukumomin tsaro da suka dace domin ci gaba da bincike.
You must be logged in to post a comment Login