Labarai
NDLEA ta gano wata katuwar Gona da ake noman tabar wiwi a Kano
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano ta gano wani manomin tabar wiwi da gonar da ake nomata a nan Kano.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a nan Kano Isah Likita Muhammad, ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na safiyar Yau litinin 22 ga watan Maris din 2021.
Isah Likita, ya kuma ce zuwa yanzu suna fadada bincike kafin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
Akwai tarin kalubale wajen yaki da kayan shaye-shaye musamman yadda masu safarar ke amfani da motocin daukar kayan Masarufi da na gini wajen shigo da Miyagun Kwayoyi cikin Jihar Kano,” inji Isah Likita.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya ruwaito cewa kwamandan hukumar ta NDLEA a nan Kano Isah Likita Muhammad, na cewa ba zai saurarawa duk jami’insa da aka samu da karbar na goro ko alaka da masu safarar miyagun kwayoyi ba.
You must be logged in to post a comment Login