Labarai
NSCDC ta tabbatar da mutuwar matafiya 11 sakamakon kifewar kwale-kwale

Hukumar Tsaro ta Civil Defence reshen jihar Jigawa, ta tabbatar da mutuwar matafiya 11 sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya afku a Karamar Hukumar Ringim.
Mai magana da yawun hukumar na jihar, Badruddeen Tijjani Mahmoud, ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Freedom Radio.
Ya ce, lamarin ya faru ne a kauyen Malamawa da ke yankin yan Dutse a Karamar Hukumar Ringim, inda kwale-kwalen da ke dauke da fasinjoji ya kife tare da nutsuwa a ruwa.
You must be logged in to post a comment Login