Labarai
Oyo: NUT ta umarci malaman firamare da sakandare su tsunduma yajin aiki

Kungiyar malamai ta kasa ta umarci malaman makarantun firamare da sakandare a jihar Oyo su shiga yajin aiki daga yau Litinin har sai abin da hali ya yi.
Umarnin ya fito daga shugabancin ƙungiyar na ƙasa a matsayin nuna damuwa kan ci gaba da tsare malamai da kuma ɗaliban da aka sace, wanda zuwa yanzu ba a da tabbaci kan lokacin da za a kuɓutar da su ba.
A cewar ƙungiyar, ci gaba da tsare ɗaliban da malaman na ƙara haifar da fargaba a tsakanin malamai tare da sa iyaye yin baya-baya da tura ƴaƴansu zuwa makaranta.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa lamarin ya zo ne bayan umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bayar na ɗaukan jami’an tsaron gandun daji 1,000 domin taimakawa wajen kuɓuto da malamai da ɗaliban da aka sace.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar reshen Oyo Kwamared Hassan Fatai ya sanyawa hannu, NUT ta ce an ɗauki matakin domin jawo hankalin hukumomi su gaggauta ruɓanya ƙoƙarinsu na ganin an sako waɗanda akai garkuwa da su ba tare da ɓata lokaci ba.
You must be logged in to post a comment Login