Labarai
Yusuf Tuggar ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani na gwamnan Bauchi

Tsohon Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani na gwamnan APC a Jihar Bauchi, inda tsohon gwamna Mohammed Abubakar ya samu tikitin takarar jam’iyyar.
Tuggar ya ce ya shiga zaben ne da fatan za a gudanar da sahihin zabe mai gaskiya da adalci wanda kowa zai amince da sakamakonsa.
Tuggar ya yi zargin cewa Ministan Lafiya, Ali Pate, ya taka rawa wajen kakaba wasu ‘yan takara a APC ta Bauchi. Ya kuma yi ikirarin cewa Pate ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin rokon kada a ba shi damar zama dan takarar gwamna.
Ya kara da cewa irin wadannan matakai na rashin adalci ne ke haddasa ficewar wasu fitattun ‘yan siyasa daga APC. Tuggar ya bukaci Shugaba Tinubu da ya binciki lamarin tare da magance abin da ya kira rashin dimokuradiyya da ke gudana a jam’iyyar a jihar Bauchi.
You must be logged in to post a comment Login