Labaran Kano
NDLEA ta kama masu fataucin miyagun kwayoyi a Kano
Hukumar hana sha da fataucin miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Emmanueal Okasia, kan zargin safarar tabar Wiwi daga kudancin Kasar nan zuwa nan Kano, da kuma wani mai suna Anas Wada Adamu, da shi ma ke zargi da sayar da tabar Wiwi a Karamar hukumar Kura.
Kwamandan hukumar a nan Kano Dakta Ibrahin Abdul ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da Freedom Rediyo a shelkwatar hukumar dake kan titin zuwa Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
Ibrahim Abdul, ya kuma kara da cewar hukumar ta tashi tsaye wajen kawo karshen masu safarar miyagun kwayoyi a kano, yana mai cewa za su gurfanar da wadanda suka kama a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.
Daya daga cikin wadanda ake zargin Emmanueal Okasia ya tabbatar da cewar hukumar ta kama shi da buhunan tabar Wiwi fiye da ashirin, da yake kokarin sayarwa a nan Kano.
Shi ma dayan mai suna Anas Wada Adam, da ake zargin yana fakewa da sana’ar wasan buga Sunuka yana sayar da tabar Wiwin, ya bayyana cewa abokinsa ne ya ba shi tabar don sayarwa.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya rawaito cewar kwamandan hukumar ta NDLEAa nan Kano Dakta Ibrahim Abdul na yabawa masu baiwa hukumar bayanan siri wanda hakan ke taimakawa kokarin hukumar.