Labarai
NDLEA ta kwace miyagun kwayoyi na Naira biliyan 80 cikin watanni 3 – Buba Marwa
Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) Burgediya janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya, ya ce jami’an hukumar sun samu nasarar kwace miyagun kwayoyi a sassa daban-daban na kasar nan cikin watanni uku da suka gabata da kudinsa ya kai naira biliyan 80
Burgediya janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya ya bayyaa hakan ne lokacin da ya ke tattaunawa da mai rikon mukamin sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan Usman Alkali Baba wanda ya kai masa ziyara ofishinsa da ke Abuja
Buba Marwa wanda ke cika kwanaki dari da fara aiki a matsayin shugaban hukumar ta NDLEA a jiya laraba, ya ce, sun kama miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai sama da kilo miliyan biyu cikin wannan wa’adi na watanni uku.
‘‘Mun kuma kama mutane 2,100 da laifuka daban-daban da suka shafi sayar da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi yayin da muka samu nasara a shari’u 350 da muka shigar a kotuna’’ a cewar Buba Marwa